An Kama Wani Likitan Da Ya Yada Cutar Sankarau A Mexico

Yan sandan Mexico

‘Yan sandan Mexico sun tsare wani likita da ake zargi da amfani da gurbataccen magani da ake zaton ya haddasa barkewar wani nau’in cutar sankarau a jihar Durango dake arewacin kasar.

Lamarin dai ya faru ne bayan da cutar ta kashe akalla mata 35 a cikin ‘yan watannin nan.

An kwantar da wasu mutane 79 a asibiti masu dauke da alamomin kamuwa da cutar.

‘Yan sandan sun kama likitan wanda ya kware a fannin allura a dakin tiyata da safiyar jiya Talata da laifin yin aiki ba bisa ka’ida ba ciki har da sake yin amfani da wasu magunguna a wani asibiti mai zaman kansa inda yake aiki.

Sai dai ba a bayyana sunan likitan ba.