WASHINGTON, D.C. —
Yan sanda a yankin Gibraltar, mallakin kasar Burtaniya, sun kama wani tankin mai, mallakin kasar Iran, wanda ake kyautata zaton ya na dauke da danyan mai daga kasar Siriya, wanda hakan ya saba ma takunkumin da Tarayyar Turai ta kakaba ma ta.
Wannan ne karon farko da wata kasa ta tarayyar Turai ta dau wani mashahurin mataki na ganin cewa an kiyaye takunkumin.
Hukumomin Gibraltar, tare da taimakon sojojin ruwan Burtaniya, sun kama jirgin ruwan mai suna Grace 1 da safiyar jiya Alhamis a wani sashi na tekun Bahar Rum, inda Burtaniya da Spain kowacce ke ikirarin na ta ne.