Rahotanni da dama na cewa Jami'an hukumar tsaron Najeriya na farin kaya (DSS), sun kama shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu bisa wasu zarge-zarge.
Kakakin shugaban na EFCC ya shaida wa gidan talabijin na Channels da faruwar lamarin, sai dai ya jaddada cewa gayyata ce kawai Magu ya je amsawa.
A cewar jaridar Sahara Reporters an kama Magu bisa zargin cewa yana da gidaje 4, sa'anan yana aikewa da kudade zuwa kasashen waje tare da taimakon wani.
A cewar wata sanarwa wacce hukumar ta DSS ta fitar a shekarar 2016, ana zargin Magu da zama cikin wani gida wanda ya kai miliyan 40 wanda wani Umar Mohammed ya siya.
Sanarwar ta kuma jaddada yadda Magu ke tafiya akai-akai cikin wani jirgin sama mallakin wannan mutumin Umar Mohammed.
Masana sun bayyana cewa a ka'idar aikin gwamnati a najeriya, duk wanda zai yi rikon kwarya a kowace hukuma, bai kamata ya wuce watanni shida ba.
Shi dai Magu ya yi shekara 5 yana rike da wannan mukamin kuma sau biyu ana aikewa da sunansa ga majalisar dattawa amma suka ki tantance shi.
A kwanakin baya hukumar ta DSS ta bayyana cewa a ganinsu Magu ba zai iya rike EFCC yadda ya kamata ba saboda "yadda ya ke da hannu a sha'anin cin hanci da rashawa shi kansa."