An Kama Mutane 12 Kan Zargin Sace Tagwayen Zamfara

'Yan tagwayen jihar Zamfara da aka yi garkuwa da su a watan Oktoba (Hoto: Daily Nigerian)

Rundunar 'yan sanda ta ce har yanzu tana neman wasu mutane biyu da suke da hannu dumudumu a sace 'yan matan.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, rundunar ‘yan sandan kasar sun cafke mutane 12 da ake zargi na da hannu a garkuwa da wasu ‘yan tagwayen mata wadanda aka sace su a lokacin ana shirin aurensu.

An sako tagwayen ne a watan Nuwamban da ya gabata.

Kafofin yada labarai a Najeriya da dama sun ruwaito cewa Kakakin rundunar ‘yan sandan kasar DCP Jimoh Moshood, ya gabatar da mutanen da ake zargi da hannu a hedkwatarsu da ke Abuja.

Moshood ya fadawa manema labarai cewa an cafke mutanen ne a wasu yankunan jihar Katsina da Zamfara, inda suka amsa laifin cewa suna da hannu a yin garkuwa da tagwayen kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

Jaridar Vanguard ta ruwaito kakakin na ‘yan sanda yana cewa, mutanen da aka kama, sun amsa laifin cewa sun karbi naira miliyan 15 kafin su saki tagwayen ‘yan matan.

Rundunar 'yan sanda ta ce har yanzu tana neman wasu mutane biyu da suka ce da hannu dumudumu a sace 'yan matan.

A watan Oktoban da ya gabata, aka yi garkuwa da Hassana Bala da Hussaina Bala, a lokacin suna kan hanyarsu ta zuwa raba katin gayyatar daurin aurensu.

A ranar 21 ga watan Oktoban shekarar nan, aka sace ‘yan matan biyu a kauyen Dauran da ke karamar hukumar Zurmi a jihar ta Zamfara.

Wadanda suka yi garkuwan da su, sun yi barazanar halaka su idan ba a biya kudin fansar da suka nema ba.