An Kama Mayakan Niger Delta Fiye da 1000

Shugaban rundunar tsaro ta kasa Air Marshal Alex Badeh, ya ziyarci hedkwatar rundunar gamayyar jami’an tsaron yankin Niger Delta, JTF, dake birnin Yanagua a jihar Bayelsa.

Rundunar Sojojin Najeriya ta samu bayanai na siri kan cewar wasu matasa a yankin Niger Delta, na shirin sake daukar makamai domin fara sabon ta’annati a yankin na Niger Delta, masamman na kai hare hare a harabobin da ake aiyukan hakar danyen mai inda kuma ya tabbatar da cewar rundunar tsaron Najeriya, baza ta sake bada dama ba na dawowa da ta’annati a yankin mai arzikin mai.

Shugaban rundunar ta JTF, Manjo Janar Eje Ateweye, yace “ muna kokarin kaddamar da matakan da Gwamnati ta fito dasu domin tunkaran wadannan kalubale, kuma maganar da nake yi mun kama masu laifi sama da dubu daya kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gurfanar dasu gaban kotu, sannan kuma muna ci gaba da gudanar da sintiri kan masu satar danyen mai a yankin.”