An Kama Mallaman Makaranta 46 masu takardun jabu a Nijer

Hukumomi a jihar Maradi ta jamhuriyar Nijar sun tabbatar da kamewa da tsare wasu malaman makarantun boko na jabu arba’in da shida da ake zargi da laifin anfani da takardun jabu na kamala karatun jami’a.

Wannan lamari ya biyo bayan cece kuce na tsawon lokaci tsakanin kungiyar hadakar malumma na kasar da hukumomi game da tantance takardun daukar malamai aiki.

Mallam Zakari Umaru shine Gwamnan jihar Maradi kuma ya tabbatarwa manema labarai da kama malumman na jabu, inda yake cewar tuni aka aike da sunayen malumman zuwa kotu.

A nata bangare kungiyar hadakar malummar jihar Maradi tace ba zata goyi bayan duk wani mallamin dake aiki da takardun jabu. Shugaban kungiyoyi Mamman Mani yace malluman da aka samesu da takardun jabun suna hannu hukuma.

Your browser doesn’t support HTML5

HUKUMOMIN MARADI SUN KAMA MALLAMAN JABU