An Kama Maharan Da Suka Kashe Wani a Nijar

Wasu al'ummomi a Njiar yayin da suka fito nuna farin cikin kama wadannan maharan

Kasa da sa'o'i 24 da wadansu mahara suka yi harbe-harbe a Birnin Konni da ke Jamhuriyar Nijar, dubunsu ta cika.

Jami'an tsaro ne suka samu nasarar cafke su, lamarin da yayi wa al'ummomin birnin dadi.

Saboda murnar wannan lamarin dai, mutane da dama suka hallara a offishin ‘yan sanda domin kai musu jinjina da neman ganin wadanda aka cafke.

Wasu al'ummomi a Njiar yayin da suka fito nuna farin cikin kama wasu mahara da aka yi


A madadin hukumomin bariki da na gargajiya Docteur Sumaila Assumane, magajin garin birnin na Konni ya yi wa al'ummar garin jawabi tare da yi musu godiyar goyon bayan da suka nuna wa jami'an tsaro.


Jiya da safe ne dai aka gano cewa mutum bakwai ne suka jikkata sakamakon harin da maharan suka kai a daren shekaranjiya.

A yanzu mutum hudu ne aka cafke, har da wata mace, an kuma kwace makamansu da ma mai basu makaman inji shugaban gundumar Birnin Alhadji Abba Lele.

A cewar mazauna birnin, kwanciyar hankali ya dawo a yayin da kowa ya koma bakin aiki kamar yadda aka saba.

​A daren shekaranjiya ne maharan suka kai wa 'yan canji hari, tare da harbe-harben bindigoginsu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum daya, da kuma raunata wasu da dama.

Ga rahoton a sauti daga bakin wakilinmu Harouna Mamane Bako.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kama Maharan Da Suka Kashe Wani a Nijar