‘Yan sanda a Jamhuriyar Nijar sun cafke wasu masu safarar miyagun kwayoyi lokacin da suke kokarin ratsa kasar da nufin isar da wasu bahunhunan kwayoyin Tramadhol zuwa kasar Libya.
Binciken da jami’ai suka gudanar a wata motar da ta fito daga kasar Burkina Faso ne dauke da lodin dankalin turawa ya ba da damar gano wasu bahunhunan shake da kwayar Tramadhol da aka fi sani da Tramol kimanin kilo 25000.
A lokacin kamen, daya daga cikin masu safarar na jiran isowarsu Yamai domin aikawa da su zuwa Agadez inda a can ma aka gano wasu kayan na daban in ji kakakin hukumar ‘yan sanda, Cap. Mainasara Adili Toro, a lokacin da ake gabatarwa manema labarai wadannan diloli.
Bayanai sun yi nuni da cewa masu safarar na ratsa kasar ta Nijar ne domin isar da hajarsu zuwa kasar Libya inda sojan sa-kai ke gobza fada a rikicin shugabancin da kasar ke fama da shi.
Hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewa za ta damka wadanan mutane a hannun hukumomin shara’a don ganin an gurfanar da su a gaban kuliya.
Ko a makon jiya ‘yan sanda sun gargadi jama’a akan bukatar matsa kaimi wajen yaki da miyagun kwayoyi bayan da suka cafke wasu ‘yan fashin da bayanai ke nuni da cewa amfani da kayan maye ne mafarin da wadannan matasa suka rungumi dabi’ar kisan kai da kwacen dukiyoyi bayin Allah.
Saurari rahoton Sule Mumuni Barma daga Yamai:
Your browser doesn’t support HTML5