An kama shi ne tare da wasu mutum bakwai, bayan da aka zarge su da laifin keta sabuwar dokar nan ta tsaro da China ta sakawa yankin a baya-bayan nan.
Jaridar Apple Daily wacce ke karkashin kamfanin Lai mai suna Next Digital ya wallafa cewa an kama Lai mai shekara 72 bisa zarginsa da laifin hada kai da wata kasar waje.
Jaridar ta kara da cewa an kama daya daga cikin ‘ya’yansa. ‘Yan sanda a Hong Kong sun ce sun kama wasu maza bakwai masu shekaru tsakanin 39 zuwa 72, amma ba su bayyana sunayensu ba.
Apple Daily ta kasance daya daga cikin jaridun da aka fi karantawa a Hong Kong, sakamakon hakan ne wasu da Reuters ta zanta da suka bayyana cewa dama sun san wannan ranar za ta zo.
"Rufe Apple Daily da kuma murkushe dukannin jaridu masu fadin albarkacin bakinsu shi ne abinda ake kokarin yi," a cewar daya daga cikinsu.
Sa'o'i bayan kama Lai, fiye da jami'an 'yan sanda 200 sun kai wani samame a hedikwatar kamfanin nasa na Next Digital Company.