An shigar da wata kara a kotun kolin India dake kalubalantar matakin gwamnatin kasar na korar yan kabilan Rohingya da suka kai dubu dari hudu da suka arce daga Myammar.
WASHINGTON DC —
Kotun kolin ta kasar India ta fara sauraren wannan karar a yau Litinin.
A wata sanarwa da gwamnatin ta aikewa kotun tana cewar yan Rohingya baki ne da basu da izini kuma wasu acikinsu na iya zama babban barazana ga tsaron kasar India.
Lauyan dake wakiltan yan Rohingya yace dokokin India sun bada daman daidaita yancin da kuma walwala ga kowane mutum, har ma da wadanda bay an kasar ba.
Kotun zata ci gaba da sauraren wannan karar a wata mai zuwa.