An Kakkabo Jirgin Yakin Rasha Kan Iyakar Turkiya Da Syria

This frame grab from video by Haberturk TV, shows smoke from a Russian warplane after crashing on a hill as seen from Hatay province, Turkey, Nov. 24, 2015.

A yau Talata, kasar Rasha ta ce an kakkabo daya daga cikin jiragen yakin ta mai lamba SU-24 a kan iyakar Turkiyya da Syria

Amma hukumomin kasar sun ce, harbe-harbe daga kasa ne ya yi sanadin faduwar jirgin.

Sai dai hukumomin kasar Turkiyya sun ce, jirginsu mai Lamba F-16 ne ya harbor jirgin na Rasha, a lokacin da ya ketara iyakar kasar, bayan kashedi da akawa matukan jirgin har sau 10 na cewa su fice cikin mintina biyar.

Sai dai ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta musanta hakan, tana mai cewa, jirgin bai fice daga yankin kasar Syria ba.

Wani hoton bidiyo da aka nuna, ya dauko wasu matukan jirgi biyu suna ficewa a cikin lemar sauka daga jirgi cikin gaggawa, inda daga baya, ‘yan tawayen Syria suma suka fitar da wani hoton bidiyo da ya nuna cewa daya daga cikin matuka jirgin ya mutu.

Yayin da hukumomi a Kremlin ke kwatanta lamarin a matsayin wani babban al’amari, sun kuma tabbatar da ficewar matukan daga cikin jirgin, tare da cewa ba ta san inda suke ba a yanzu.