Duk da dai jami’ai sunce wannan kame bai da wata alaka da takardar umurnin hana wasu baki shigowa kasar nan da shugaba Donald Trump ya rattaba ma hannu kwanakin baya.
Mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka, Gillian Christensen, ta fadawa Jaridar Washington Post cewa an kai sumamen ne domin kama bakin hauren dake aikata laifuffuka, tana mai fadin cewa wannan abu ne da aka saba yi.
Christensen ta fadawa jaridar cewa, “Muna maganar mutane ne da suke barazana ga lafiyar al’umma, barazana ga tsarin ayyuka na hukumar shige da fice,”
Mai Magana da yawun hukumar shige da fice da kuma Fasakwauri (ICE) a takaice Jennifer Elzea ta fadawa kamfanin dillancin labarai na Faransa“ Dalilin wannan kame baisha bambam ba da yadda jami'an ICE ke gudanar da ayyukansu na yau da kullum.”
Anyi wannan kame ne a jihohi akalla shida, inda aka yi kame cikin biranen da suka hada da Atlanta da Chicago da New York da Los Angeles inda aka kama fiye da mutane 160 a cikin wannan Makon.