Bana aka yi rabin wa’din da aka tsayar na yiwa dukkan yara da manya alluran rigakafin cututtuka domin ceton rayukansu. Domin kuwa shekaru shidda da suka shige kasashe dari da casa’in da hudu suka rattaba hannu akan wata yarjejeniya ko kuma shirin yin alluran rigakafin cututtuka.
Buri wannan mataki shine yiwa miliyoyin jama’a alluran rigakafin cututtuka kan shekara ta dubu biyu da ashirin lokacinda wa’adin shirin zai cika.
Dr Flavia Bustreo itace mataimakiyar direktan shirin kula da lafiyar iyali da mata da yara na kungiyar lafiya ta duniya. Dr Bustreo tace alluran rigakafi sune makamai kiwon lafiya mai karfi da suke da shi a halin yanzu na yaki da cututtuka.. Tace shekaru talatin da biyar da suka shige, kimamin yara miliyan goma sha uku suka yi hasarar rayukansu skamakon cututtukan da za’a iya rigakafin su da alluran rigakafi.
Tace Alhamdullilahi, kodayake an rage yawansu zuwa miliyan shidda, amma miliyan shidda ya yi yawa. Tace sai gashi a yau kimamin kashi tamanin da biyar daga cikin dari na yara ake yiwa alluran rigakafin bakon dauro da sauran cututtuka, to amma tace akwai karin yara da suke bukatar wadanna alluran rigakafin.