An Kai Munmunan Hari A Birnin Tripoli, Na Kasar Libiya

Hukumomi a kasar Libya, sun tabbatar da cewar wasu mahara sun abkawa ma’aikatar harkokin wajen kasar da ke Tripoli a yau Talata, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3.

Harin ya hada har da wani dan kunar bakin wake, lamarin da ya haifar da tashin hayaki. Ya zuwa yanzu, babu wanda ya dauki alhakin wannan hari.

Kasar Libya ta sha fama da rikicin siyasa, tun bayan da aka kifar da gwamnatin dadadden shugabanta Mohammad Gadhafi, aka kuma kashe shi a shekarar 2011.

Sanadiyar kawar da Gadhafi, an samu gwamnatoci masu kishi da juna, da kuma rarrabuwar kawunan sojojin kasar a birnin na Tripoli da gabashi kasar, inda aka yi ta fafutukar karbe ikon arzikin man fetur din kasar.

A daya bangare kuma, wannan rikicin sun bai wa ‘yan ta’addan kungiyar IS matsugunni na gudanar da ayyukansu.