An kai Harin Kunar Bakin Wake Wani Masallacin Yan Shi'a A Afghanistan

Afghan Municipality workers collect shoes of victims in front the Baqir-ul Ulom mosque after a suicide attack, in Kabul, Afghanistan, Nov. 21, 2016.

Jami’ai a Afghanistan sunce Bam din da dan kunar bakin wake ya tayar a Masallacin Yan Shi’a a Kabul a Yau Litinin ya kashe sama da mutane 30 ya kuma jikkata wasu 85.

Dan kunar bakin waken ya shiga Masallacin Baqir ul Olum da yake shake da jama’a a yayin da ake gudanar da biki, ya tashi Bam din da suke daure a jikinsa a tsakiyar masu gudanar da Ibada.

Janar Faridoon Obaidi, Shugaban bangaren masu binciken Manyan laifuffuka a Kabul, ya fadawa manema labarai cewa duk wadanda abin ya shafa fararen huluna ne. Jami’an Yan sanda sunce sama da mutane 50 ne suka ji rauni.

Shugaban kasa Ashraf Ghani yayi Allah wadai da wannan aika aika yace “Abinda ba za’a iya yafewa bane” sannan aikine na Makiya Afghanistan masu burin raba kabilun dake Afghanistan.

Babban Jami’i mai zartaswa Abdullah Abdullah shima yayi Allah wadai da wannan hari inda yace “An kai hari kan wadanda basu ji ba, ba su gan iba da suka hada da yara a waje mai tsarki, wannan laifin Yaki ne, kuma ya sabawa addinin Musulunci”.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin wannan zubar da jini.

Mai Magana da yawun Kungiyar Taliban ya fada a cikin wani sako da ya turawa manema labarai inda yace Kungiyar Taliban bata da hannu a cikin wannan aika aika.