An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Wajen Bikin Aure A Iraqi

Wasu da suke juyayi bayan harin

Jami’ai a Iraqi sun ce wasu ‘yan kunar bakin wake su biyar, sun kai hari a wajen wani bikin aure, inda suka halaka mutane 15.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa, ya ruwaito cewa mutane 20 sun jikkata a harin, wanda aka kai shi ranar Lahadi a garin Ain-al-Tamer da ke da tazarar tafiyar kilomita 50 daga birnin Karbala na ‘yan Shi’a.

Daya daga cikin manyan jami’an tsaron yankin mai suna Qais Khalaf, ya ce “’yan kunar bakin waken, suna dauke ne da nau’in bindigar nan mai suna Kalashnikovs da ake kerawa a Rasha, da gurneti-gurneti, kuma daya daga cikinsu ya tarwatsa kansa, yayin da sauran kuma jami’an tsaro suka harbe su har lahira.”

Sai dai jami’an sun ce ya zuwa yanzu babu wani da ya dauki alhakin kai wannan hari, koda ya ke a cewarsu, ire-iren wadannan hare-hare, kungiyar IS ce ke kai su.