Akalla mutum daya ya rasa ransa wasu mutane hudu ko wadanda suka fi haka sun sami raunuka, sakamakon wani hari da wuka da aka kai a birnin Paris jiya Asabar.
Tuni kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai wannan hari, kamar yadda ta kamfanin dillancin labarunta ya bayyana. Kungiyar ta jinjinawa maharin wanda har zuwa yanzu ba 'a bayyana sunansa ba, duk da cewa, 'Yansanda kasar sun gama da shi, a inda ya kai harin.
Hukumomin tsaron kasar suka ce an kai harin ne a gunduma ta biyu a birnin na Paris, wacce a dai dai lokacin, take shake da mutane wadanda suke shirin zuwa wuraren shakatawa.
Mai gabatarda kara a birnin na Paris Francois Molins, ya gayawa manema labarai cewa, mutumin yayi kabbara lokacin da yake kai harin. Molins yace 'Yansanda zasu kaddamar da bincike a zaman harin ta'addanci.
Shugaban Faransa Eammanuel Macron, ya fada ta shafinsa na Twitter cewa, "ba zamu bada dai-dai da inchi daya ba ga makiyan 'yanci ba."