Na’urar garkuwa daga manyan makamai ta tare roka daya da aka harbo daga Gaza, a cewar rundunar sojin Isra’ila.
An kai Netanyahu da matar sa Sara a wata maboya da ke kusa a yayin da rokar ta ke kara. Daga bisani ya koma domin iyar da jawabin sa a gangamin.
Shugaban na Isra’ila yana yakin neman zabe ne gabanin zaben fitar da gwani a yau Alhamis, inda zai fafata da dadadden abokin adawar sa Gideon Saar, a shugabancin jam’iyyar Likud.
Haka kuma yana fuskantar babban zabe na 3, shekara daya bayan sakamakon zaben watannin Afrilu da Satumba, sun nuna zai sake gwabzawa da Benny Gantz, a yayin da cikin su ba wanda ya sami isassun kuri’un da zai kafa gwamnati.
A watan da ya gabata, an tuhumi Netanyahu da laifin zamba, cin hanci da cin amanar kasa a kararraki 3 daban-daban. To amma ya jaddada musanta dukkan zarge-zargen.