An Kai Hari Akan Asibitin Sojin Afghanistan a Kabul

Akalla mutane 30 suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata a wani hari da aka kai kan asibin sojojin Aghanistan dake birnin Kabul.

Wasu mayakan ‘yan ta’adda da suka yi shigar burtu suka fito a matsayin likitoci sun kai hari a babban asibitin sojin kasar Afghanistan dake birnin Kabul a yau Laraba, inda suka hallaka akalla mutane 30, kana suka raunata wasu da dama, a cewar Ma’aikatar tsaron kasar.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce harin an fara shi ne da kai harin kunar bakin wake a wata mota a kofar shiga asibitin mai suna Sardar Mohammad Daud Khan, wanda kuma yake da gadajen kwanciyar guda 400.
Daga baya kuma sai maharan dauke da manyan makamai, da gurneti da, riguna da bama-bamai suka kutsa kai cikin ginin asibitin.
Rahotannin sun ce maharan sun kaikaici masu jinya da kuma ma’aikatan asibitin kafin daga baya dakarun kasar su zo su harbe su.
Tuni dai kungiyar IS ta dauki alhakin wannan hari.
Wadanda suka shaida lamarin sun kara da cewa motacin daukan marasa lafiya suna ta zirga-zirga, suna kai wadanda suka ji rauni asibitin Wazir Akbar Khan, kuma mafi yawansu ma’aikatan asibitin da aka kai harin ne.