Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da kai wani hari, duk da yake ta musanta rahotannin rasa rayuka, da kuma na cewar maharan sun tafi da wasu daliban makarantar.
Lamarin ya auku ne da misalin karfe 9 na daren jiya, lokacin da ‘yan bindigar akan Babura suka kai farmaki a wannan makarantar sakandire ta ‘yan mata dake garin Moriki, a yankin karamar hukumar mulki ta Zurmi a jihar Zamfara, inda suka samu yin awon gaba da wasu mutane kimanin su 6 a makarantar.
SP Muhammad Shehu shine kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara, shi ya bayyana hakan.
To sai dai rahotanni sun bayyana cewa an samu tabbatattun bayanai na yiwuwar kai wannan harin tun da safiyar jiya, kuma tuni da aka sanar da jami’an soji da ke yankin kafin zuwan ‘yan bindigar, a cewar shugaban karamar hukumar mulki ta Zurmi, Dr. Ahmed Bawa Moriki.
Yankin na karamaru hukumar Zurmi dai na daga cikin yankunan da suka dade suna fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga, da satar jama’a a jihar ta Zamfara, duk kuwa dakarun sojin sama da suke cewa suna luguden wuta da fatattakar maharan.
Your browser doesn’t support HTML5