An Kai Hari a Jamus

Inda aka kai wami harin wuka a farkon makonnan a Jamus

Mutanen da ba a san adadinsu ba sun samu raunuka bayan da ‘yan sandan Jamus suka ce an yi harbe-harbe a wasu shaguna cinikayya, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka yi tururwa zuwan wurin.

“Ana kai wani dauki a wata cibiyar kasuwanci.: ‘Yann sandan Munich suka rubuta a shafinsu na Twitter, ba tare da sun fadada bayanin ba.

Ya zuwa yanzu bayanai ba su bayyana wanda ya kai harin ba.

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa an samu mutuwa a harin, kana wasu da dama sun jikkata bayan wani harbi da aka yi a kantunan Olympia da ke birnin Munich.

A daidai lokaci da ake hada wannan rahoto, 'yan sandan sun ce ba su san yawan 'yan bindigar da suka kai harin ba, kuma ba a san inda su ke labe ba.

Koda ya ke wasu wadanda suka shida lamarin sun sun ga wasu 'yan bindiga uku.

Wannan harin da aka kai na zuwa ne mako guda bayan wani hari da wani dan gudun hijra dan asalin Afghanistan mai shekaru 17 ya kai da da adda akan wasu fasinja a wani jirgin kasa a Wurzburg.