An Kai Har Cikin Dare Ana Kada Kuri’a A Wasu Rumfunan Zabe A Abuja

Kada kuri'a da dare

Wasu rumfunan zabe a babban birnin tarayyar Najeriya sun kasance da dogayen layuka har cikin daren Asabar yayin da masu kada kuri'a su ke jira don su kada kuru'unsu.

Duk da na’urar tantance masu kada kuri’a da aka tanada don zaben bana, an bi tsarin gargajiya da aka saba na daukar kuri’a daya bayan daya da mutane kan kidaya da kansu har sai an gama kirga kuri’ar da kowane dan takara ya samu.

A bayyane ya ke yadda magoya baya kan nuna farin cikinsu ta hanyar sowa in su ka ji dan takararsu ke kan gaba a rumfar zabe.

Zaben shugaban kasa a Abuja

A mazabar AYA da ke Abuja, inda dan takarar Labour ya lashe da kuri’u 245, daga na sai mai bi ma sa baya Bola Tinubu wanda ya samu kuru'u 67, magoya baya sun bayyana farin cikinsu saboda akalla dai sun yi nasara a mazabar.

Isra’il Sunday, na daga cikin masu mara wa Peter Obi na jam'iyyar Labour baya, wanda ke tunanin nasarar da mazabarsa ta samu na nuna in dai ba Obi ne aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zabe a kasa baki daya ba, to an yi wani abu da ya saba ka’ida.

Zabe a Abuja

Shi kuma Ibrahim Zubairu, daya daga cikin masu mara wa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP baya cewa yayi dama akasarin mutanen da ke zabe a rumfar magoya bayan Obi ne.

Sai dai wani matashi mai suna Ibrahim Umaru, ya ayyana cewa ya ga ana raba kudi don zabar wani dan takara amma shi ya ce ba zai saida 'yancinsa ba ya koma yana hamma tsawon shekara hudu.

Za a bude dakin tattara sakamakon zabe na kasa da fara ayyana sakamako a Lahadin nan, lamarin da ka iya kai wa zuwa ranar Litinin ko ma gaba in aka yi la’akari da abinda ya faru a zaben baya.

Saurari rahoton Nasiru Adamu Elhikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kai Har Cikin Dare Ana Kada Kuri’a A Wasu Rumfunan Zabe A Abuja