A cigaba da fatattakar 'yan bindiga masu takura tsirarun jinsi da mabiya wasu addinai a Masar, sojojin kasar sun ce sun hallaka 'yan bindiga 19 masu alaka da kashe Kufdawa da aka yi ranar Jumma'a.
WASHINGTON D.C. —
Kasar Masar, yau Lahadi, ta ce ta kashe wasu 'yan bindiga 19, wadanda ake zargin su na da alaka da masu tsattsauran ra'ayin nan da su ka kashe Kufdawa 7 ranar Jumma'a, yayin da su ke kan hanyarsu ta zuwa wata majami'a a lardin yankin tsakiyar Minya.
Ma'aikatar Cikin Gidan kasar ta Masar ta ce an hallaka 'yan bindigar ne a wata musayar wutar da aka yi da su a hamadar da ke yammacin lardin na Minya. Amma ba ta bayyana lokacin da aka yi musayar wutar ba.
Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai hari kan Kirista Kufdawan, to amma ba da gabatar da shaida ba.
Kirista dai kashi 10% ne na adadin mutanen kasar Masar masu yawan miliyan 100. Sun dade su na korafin kuntata masu da ake yi.