Janar Thomas Cirillo Swaka ya fitar da wata takardar bayani jiya Litini, wadda a ciki ya shelanta da kansa a matsayin Chairman kuma Babban Kwamandan kungiyar national Salvation Front.
Nan take dai ba a san karfin wannan kungiyar ba, ko idan za ta hade da kungiyar Sudan People's Liberation Army, kungiyar 'yan tawayen da ta shafe shekaru uku ta na fafatawa da gwamnatin Kiir.
Shirin Muryar Amurka na Turanci mai suna South Sudan in Focus ya samu kofin bayanin na Cirillo, wanda ya zargi gwamnatin Kiir da kwace iko da dukiyoyi don kawai amfanar 'yan kabilarsa ta Dinka, kuma ta yadda ake kwarar sauran kabilun da su ma su ka taka rawa wajen wajen kwato 'yanci daga Sudan.
Wasu sassan bayanan kuma sun zargi gwamnatin Kiir din da almundahana, da kasa samar da abuwan bukata ga jama'a da kuma yin watsi da bangaren noma, wanda shi ne batu na karshe cikin manyan batutuwan da ake takaddama akansu a wannan kasar, inda tsananin fari ya jefa miliyoyin mutane cikin rashin abinci.