An kafa wannan kungiya ne don mayar da hankali wajen bunkasa noma da sarrafa albasa ta hanyar samar da kudaden shiga ta fannin tattalin arzikin Najeriya.
A shekarar 2020 ne al’ummar Najeriya suka koka a kan yadda kayakin masarufi da sauran albarkatun noma suka yi tashin gwauron zabi, babu kamar na albasa da kusan a kowanne girki ake amfani da ita.
Matsalar dai ta kai ga sai gidan wane-da-wane ake amfani da albasa wajen girka abinci, kuma ana gani rikice-rikicen da ake yi a kasar da kuma ambaliyar ruwa su suka taka gagarumar rawa ga tsadarta.
Aliyu Maitasa Isa, sabon shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da masu sarrafa albasa ta kasa baki daya, ya ce kungiyar za ta hada manoman albasa da ‘yan kasuwa da masu sarrafata wuri daya, kuma hakan zai kawo babban ci gaba ga manoma da ‘yan kasuwa da kasar baki daya.
Isa Muhammad manomi ne daga jihar Gombe, ya bayyana farin cikinsa na kafa wannan sabuwar kungiya ya na mai cewa burinsa shi ne a samu iri mai kyau na albasa, da takin zamani, da kayayyakin noma.
Wani babban kalubale da manoma ke fuskanta shi ne rashin samun tallafi duk kuwa da kokarin da gwamnati ke yi wajen maida hankali ga harkokin noma a kasar, kamar yadda Alhaji Isa Adamu manomin albasa daga jihar Adamawa ya bayyana.
A bangaren gwamanti kuwa, babban sakataren ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dakta Nasiru sani Gwarzo, ya ce babban tallafin da gwamnati za ta bai wa manoma shi ne kawo musu tsarin kasuwanci na zamani da kuma tallafi karkashin bankin Industry wanda zai taimaka a ba manoma da ‘yan kasuwa bashi.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5