Ganin yadda wasu bangarorin Najeriya su ka kirkiro tsarin tsaron yanki ya sa hadakar kungiyoyin matasan arewacin Najeriya kaddamar da Kungiyar tsaro ta yankin Arewa.
Kungiyoyin da su ka kaddamar da motocin tsaro da jami'an da za su yi aiki karkashin kunyiyar mai Suna 'Shege-ka-fasa' sun ce Arewa tafi kowane bangaren Najeriya bukatar tsaro.
Alh. Nastura Ashir Sherif, dan Kwamitin amintattu ne na hadakar kungiyoyin na Arewa, kuma ya yi karin hasken kan musabbanin kafa kungiyar ta Shege Ka Fasa da cewa tsananin bukatar tsaro na kawo haka. Da yake amsa tambaya, ya ce sam ba an kafa rundunar tsaron ta Shege Ka Fasa ne don kawai a yi gasa da 'yan gudu da su ka kafa makamanciyar wannan kungiyar ba.
Rundunar yan-sandan jahar Kaduna dai ta ce ita ba ta da masaniya game da wannan sabuwar rundunar tsaro ta yanki, inji mai magana da yawunta DSP Yakubu Abubakar Sabo. Ya kara da cewa hukumar 'yan sanda za ta yi bincike ta kuma bayyana matsayinta.
Wasu masana harkar tsaro dai na ganin sakacin gwamnatin tarayya ne ya haifar da kirkirar irin wadannan kungiyoyin tsaro na yanki.
Yanzu dai abun tsayawa a gani shi ne yadda gwamnoni da sarakuranan Arewa za su kalli wannan kungiya da kuma matsayin da gwamnatin tarayya za ta bayyana.
Ga Isah Lawal Ikara da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5