An Kafa Rundunar Shiga Tsakanin Makiyaya Da Manoma A Jahar Adamawa

  • Ibrahim Garba

Kaurar Makiyaya

Ganin yadda aka kasa tsaida yawan fada tsakanin manoma da makiyaya, a jahar Adamawa an kafa rundunar shiga tsakanin manoma da makiyaya idan takaddama ta barke tsakaninsu.

Cikin kwanakin nan dai an samu tashe tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma a wasu sassan Najeriya, kuma lamarin yafi kamari a wannan lokaci da manoma ke girbe amfanin gona. Don magance wannan matsalar ne yasa wasu hukumomin tsaro a kasar tashi tsaye don gano bakin zaren.


Yanzu haka ma tuni hukumar tsaron farin kaya a kasar ta Sibil Defens ta kafa sashin rundunar na musamman da ake kira Agro Rangers dake da zaratan shiga daji don kamo miyagun iri, da kuma sashin sulhu da shiga tsakani wato Peace and Reconciliation.


Tuni dai kwalliya ta soma biyan kudin sabulu game da wannan yinkurin a jihar Adamawa, jihar da ita ma ke fama da matsalar rikicin manoma da makiyaya.
Suleiman Baba, jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar Adamawa, ya bayyana irin nasarorin da suke samu.


Rundunar tsaron dai ta kan yi amfani ne da shugabanin kungiyoyin makiyaya da kuma na manoma. Alh. Musa Usman na cikin shugabanin kungiyar Tabital Fulaku, daya daga cikin kungiyoyin Fulani a Najeriya da itama ke bada gudumawa a wannan yunkuri. Ya yi bayanin rawar da su ke takawa.

Muhammmad Baba wani manomi da shanu suka yi wa barna a Yola, ya tabo irin ta’adin da aka yi masa da kuma yadda aka sasanta ba tare da tashin hankali ba.

Ga wakilinmu a Adamawa Ibrahim Abdul’aziz:

Your browser doesn’t support HTML5

Jahar Adamawa Ta Kafa Rundunar Shiga Tsakanin Manoma Da Makiyaya