An Kafa Kwamitin Binciken Rikicin Manoma Da Makiyaya Na Numan Da Demsa

  • Ibrahim Garba

Yawan tashe-tashen hankula sun hana sojojin Najeriya sakad

Bayan jina-jinar da aka yi a yankunan Numan da Demsa na jahar Adamawa, gwamnatin jahar, wadda ta yi ta shan suka daga bangarorin biyu, ta tashi haikan wajen yinkurin kwantar da hankula ta wajen nuna masu cewa da gaske ta ke yi game da binciken musabbabin rikicin.

“Gwamnatin jahar Adamawa ta kafa kwamitin bincike game da rikicin da ya auku a kananan hukumomin Numan da Demsa a tsakanin yan kabilar Bachama da Fulani makiyaya,wanda ya lakume rayuka da kuma dukiyar al’umma masu dinbin yawa a makwanni biyu da suka gabata.

Da yake jawabi bayan rantsar da yan kwamitin binciken, Mataimakin Gwamnan jahar Adamawan, Mr Martins Babale, ya ce burin gwamnatin shi ne kare rayukan jama’a, inda ma yace kwamitin na da hurumin binciko daukacin abubuwan da suka faru, kama daga asarar rayuka, dukiya dama dalilan auku kuwan wannan rikicin.

Mataimakin gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jahar za ta yi aiki da sakamakon binciken don hukunta wadanda ke da hannu a rikicin. ‘’Gwamnati ta kadu matuka, kuma wallahi ba za ta rage wa duk wanda ke da hannu ba.Wannan gwamnati bari na kara tabbatar muku cewa za ta aiwatar da dukkanin shawarwarin da kwamitin binciken zai bada,’’ a cewar mataimakin gwamnan.

Justice Adamu Hobang mai ritaya, shi ne shugaban hukumar binciken, ya ce an dora musu nauyi babba na tabbatar da ganin cewa an yiwa kowa adalci. Don haka shugaban hukumar ya yi kira ga al’ummar da lamarin ya shafa da kowa ya bada tasa bahasi da bayanai gaban hukumar ba tare da nuna son rai ko bangaranci ba.”

Ga Ibrahim Abdul’aziz da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kafa Kwamitin Binciken Rikicin Manoma Da Makiyaya Na Numan Da Demsa