An Kafa Kwamitin Bincike Kan Harin Da Aka kai Gidan Yarin Minna

Tawagar Ministan Tsaron Cikin Gidan Najeriya Janar Abdulrahaman Dambazzau da ta je Minna ganin abun da ya faru a gidan yarin

Tawagar gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Ministan cikin gida Abdulrahaman Dambazzau ta ziyarci gidan yarin da aka kaiwa hari a Minna cikin hijar Neja domin ganin abun da ya faru tare da daukar matakan da suka dace kana ya fada cewa an kafa kwamitin binciken lamarin

Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin binciken harin da wasu ‘yan bindiga suka kai sabon gidan yarin Minna, a ranar Lahadin da ta gabata.

Ministan cikin gidan Najeriya, Janar Abdulrahaman Dambazzau mai ritaya ne ya bayyana hakan, yayinda ya jagoranci wata tawagar da ta kai ziyarar gani da ido gidan yarin jiya Litinin.

A cewarsa sun zo ne su duba abun da ya faru domin daukar matakan kaucewa sake aukuwar irin lamarin, tare da sanin inda suka yi kuskure da kuma koyon darasi.

Janar Dambazzau y ace fursinoni 210 ne suka gudu a lokacin harin, da fatan nan da ‘yan kwanaki za’a dawo dasu. Kawo yanzu sun sake kamo kimanin guda 30.

Tawagar ta ministan ta hada da shugaban hukumar gidan yari na Najeriya, Jafaru Ahmad, wanda ya ce an kai musu harin, amma bincike zai gano maharan ko su nawa ne. Zasu binciko yadda suka samu shiga gidan yarin tare da gano dalilin kasawarsu domin ya zama masu daratsi. Hakan zai taimaka wajen magance faruwar irin wannan lamarin nan gaba.

Gwamnatin jihar Neja, ta nuna damuwarta akan harin da aka kai gidan yarin. Ta kuma yi alkawarin bada tata gudummawar da ta dace domin kara tsaurara tsaro a gidan yarin, kamar yadda Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello, ya fada. Ya ce da ikon Allah irin wannan abu ba zai kara faruwa ba.

A saurari rahoton Nasiru Batsari domin karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

An Kafa Kwamitin Binciken Harin Gidan Yarin Minna - 2’ 44”