An Kafa Kamfanin Man Ja A Jahar Oyo

'Ya'yan kwakwar man ja a wata gona

Katafaren kamfanin an kafa shi ne a karamar hukumar Oluyole a jahar ta Oyo

An kafa wani katafaren kamfanin yin man ja da man waken soya da kuma man kwakwa a karamar hukumar Oluyole a jahar Oyo.

Gwamnan jahar Oyo Abiola Ajimobi ne ya kaddamar da kamfanin na yin man ja da man waken soya da kuma man kwakwa.

Bikin kaddamar da kamfanin ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin Najeriya a ciki har da ministan noma Dr. Akin Adesina wanda yayi jawabin yiwa al'ummar Najeriya kaimin rungumar noma, musamman ma na kwakwar man ja domin nan gaba kadan idan an sa himma kamar yadda ya ce man ja zai maye gurbin man fetur:

Your browser doesn’t support HTML5

Kaddamar da Kamfanin man ja a Ibadan.-1':52"

Tun da kasar Najeriya ta samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallakar Birtaniya wannan kamfanin matsar man ja, da man waken soya da man kwakwa shi ne irin sa na farkon da aka kafa a jahohi kudu maso yammacin kasar kasar Najeriya.

Wakilin Sashen Hausa a birnin Ibadan Hassan Umaru Tambuwal ne ya aiko da rahoton.