An Kafa Hukumar Sa Ido Kan Zabe A Amurka Da Turai.

Anders Fogh Rasmussen tsohon sakataren kungiyar tsaro ta NATO. Daya daga cikin shugabannin kungiyar.

An kafa wata hukuma ta kasa da kasa da zummar kawo karshen shishigin da Rasha da wasu kasashe 'yan kama-kariya suke yi a zabubbukan kasashen yammacin duniya masu bin tafarkin demokuradiyya.

An kafa wata hukuma ta kasa da kasa da zummar kawo karshen shishigin da Rasha da wasu kasashe 'yan kama-kariya suke yi a zabubbukan kasashen yammacin duniya masu bin tafarkin demokuradiyya.

Hukumar da ake kira TransAtlantic Commission on Election Integrity, ko TCEI a takaice, na karkashin jagorancin tsohon sakataren kungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen, da kuma tsohon sakataren tsaron gida na Amurka Michael Chertoff. Har sun yi taro da manema labrai ranar jumma'a, anan birnin Washington DC.

Sarsalar kafa wannan kungiya, Rasmussen ya gayawa sashen Rasha na Muriyar Amurka, shine "katsalandan da Rasha tayi a zaben Amurka a shekara ta 2016," "amma wannan bai tsaya kan Amurka kadai ba. Hakan ya shafi turai.