Yau Asabar din nan shugaban kasar Tunisia Beji Caid Essebsi yan ayyana dokar ta baci, kwanaki takwas bayan wasu yan bindiga sun kai hari wani wurin shakatawar bakin teku mai farin jini ga yan yawo bude ido yan kasashen waje, suka kashe mutane talati da takwas.
Nan da nan ba'a tantance dalilin daya sa shugaban ya ayyana dokar ta baci a wannan lokaci ba. Kamfanin dilancin labarun kasar yace wani lokaci a yau shugaban zai yiwa yan kasar jawabi ko kuma bayani akan wannan mataki.
Dokar ta bacin da aka taba kafawa a kasar da ta baiwa yan sana da sojoji iko na musamman a watan Maris din shekara ta dubu biyu da goma sha hudu aka dage ta.
Tu lokacinda aka yi juyin juya hali a kasar Tunisia lokacinda ak kashe sojoji da yan sana da dama, kasar ta fuskan karin tarzomar 'yan Jihadi.
Shugaban kasar Tunisia ya ayyana dokar ta baci a kasar yau Asabar. Shugaban ya dauki wannan mataki kwanaki takwas bayan harin da aka kai kasar.