An Kafa Dokar Hana Fita A Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda

Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda

An kafa dokar hana fita a Bauchi bayan da wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai hari a wasu sassan jihar.

Rahotanni daga jihar Bauchin Najeriya na cewa an saka dokar hana fita a wasu sassan jihar yayin da sojoji ke fafatawa da mayakan Boko Haram.

Hukumomin jihar sun ce an saka dokar ne saboda a kare rayuka da dukiyoyin mutane.

Wannan saka doka na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ke zargin cewa an saka dokar ne saboda a yi magudin zabe, saboda gwamnati mai ci ta ga 'yan adawa na samun nasaara.

Sai dai gwamnatin kasar ta musanta wannan zargi inda su ka jaddada cewa kare rayuka ake so a yi.

A jiya ne ‘yan kungiyar ta Boko Haram su ka kai hari a jihar Gombe da ke makwabtaka da Bauchin lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama yayin da ake gudanar da zabuka.

Hukumar zaben kasar ta tsawaita wa’adin kammala zaben a wasu sassan kasar zuwa yau lahadi bayan da aka fuskanci wasu matsaloli da suka shafi tsaro da jinkirin zuwan kayayyakin zabe.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kafa Dokar Hana Fita a Bauchi -3'00"