An Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Shugaban Afghanistan

A yau Lahadi aka fara gangamin yakin neman zaben shugaban kasar Afghanistan, duk da cewar akwai matsalolin rashin tsaro, da rashin tabbas ko za’a gudanar da zabe mai inganci.

Kana babu kwarin gwiwar cewar zaben zai kankama a ranar 28 ga watan Satumba.

‘Yan takara 18 ne ke neman wannan kujerar, da suka hada da shugaban kasar mai ci Ashraf Agani, da wani babban jami’i a gwamnatin tasa Abdullah Abdullah, suka shiga wannan yakin neman zaben na watanni biyu.

Jigo daga cikin ‘yan adawa shine Abdullah, wanda yake zargin gwamnati da amfani da dukiyar kasa a yakin neman zabe.

Wasu da dama kuwa suna ganin cewar ba za’a gudanar da zabe sahihi ba.

Jami’an zabe kuwa sun bata tabbacin cewar za’a gudanar da zabe cikin gaskiya da rikon amana, duk da cewar kusan rabin kasar ta Afghanistan na cikin rikicin ‘yan ta’adan Taliban.