An kaddamar da wani shirin yaki da zazzabin cizon sauro da zai ci dala miliyan 82 a Najeriya

Wata mace ana yiwa jaririnta allurar rigakafin zazzabin cizon sauro

A yunkurin shawo kan zazzabin cizon sauro a Najeriya , cibiyar inganta rayuwar kasa da kasa ta Amurka- USAID, da cibiyar kula da lafiyar Iyali ta kasa da kasa-Family Health International 360 (FHI360) da kuma sauran abokan hadin guiwa, sun hada kan kwararru a fannin kiwon lafiya domin bayyana shirin yaki da zazzabin cizon sauro na jihohi da ake kira MAPS a takaice, wanda a halin yanzu ake aiwatarwa a jihohin Ebonyi Nassarawa, Cross Rivers, Oyo , Zamfara da kuma Benue, za a kuma fara aiwatar da shirin a wata jiha ta bakwai farkon wannan shekarar ta dubu biyu da goma sha biyu.

A wajen bayyana shirin, jakaden Amurka a Najeriya, Mr. Terrence McCauley, da karamin ministan lafiya na Najeriya Dr. Muhammad Ali-Pate sun jadada cewa, har yanzu zazzabin cizon sauro shine cutar da tafi katse hanzarin mata da kananan yara a duniya baki daya.

Bisa ga cewar Dr. Pate, kasashen nahiyar Afrika suna kashe kimanin dala biliyan goma sha biyu a shekara kan cutar malariya. Bisa ga cewarshi, koma bayan da cutar malariya take kawowa yana da yawan gaske, kasancewa Najeriya tana asarar kimanin Naira biliyan dari da talatin da biyu wajen rigakafi da bincike da kuma jinyar cutar. Banda awowin da ake asara na aiki.

Darektan Cibiyar kula da lafiya ta duniya -FHI 360, a Najeriya Otto Nzapfurundi Chabikuli yace duk da fasahar tantancewa da rigakafi da kuma jinyar cutar da ake da ita, wadanda basu da tsada, zazzabin cizon sauro ya ci gaba da kasancewa cutar da take katse hanzarin mata da kananan yara a Najeriya, abinda yake haddasa talauci da rashin ci gaba da kuma rage yawan yaran dake zuwa makaranta.

Ya bayyana cewa, shirin MAPS a Najeriya shine shirin rigakafin zazzabin cizon sauro da cibiyar hfi360 take aiwatarwa, kuma wanda yafi kowanne zurfi.

Da yake kaddamar da shirin, jakaden Amurka a Najeriya, Mr. Terrence McCauley yace an tsara shirin MAPS ne domin mara bayan shirin yaki da zazzabin cizon sauro na kasa ta wajen amfani da dabarun da zasu inganta matakan da ake dauka na shawo kan cutar. Jami’in diplomasiyan yace cutar tana ci gaba da cin kudin kasashen Afrika a kalla karamin yaro daya yake mutuwa a cikin kowanne sakan uku a nahiyar Afrika.