An Kaddamar da Makon Kula Lafiyar Mata da Yara a Jihar Naija

  • Ibrahim Garba

Wani yaro na karbar rigakafi.

A wani yinkuri da masu yi su ka ce na inganta lafiyar mata da yara ne, an kaddamar da makon kula da lafiyar mata da matasa a jihar Naija.

Wakilinmu na jihar ta Naija da ya aiko da labarin, Mustapha Nasiru Batsari ya ce za a dau mako guda ne ana bau wa yara allurar riga kafi iri iri da kuma kulawa ta musamman ga mata masu juna biyu.

Babban Sakatare na Ma’aikatar Lafiya Ta jihar Naija Dr. Ibrahim Tifin ya ce daga cikin abubuwan kara lafiya da za a bai wa yara har da sinadarin vitamin A mai kara karfin ido musamman ganin yadda ciwon bakon dauro kan makantar da idon yaran.

Ya ce za a gudanar da shirin ne a dukkannin kananan hukumomi 25 na jihar tare da hadin gwiwar hukumar UNICEF da ta Lafiyar Duniya wato (WHO). Sauran magungunan sun hada da na macijin ciki. Akwai kuma wayar da kai kan halayyan inganta lafiya ciki har da muhimmancin wanke hannu musamman idan za a ci abinci. Wasu mata da su ka halarci taron sun bayyana cewa sun amfana su da ‘ya’yansu sosai.

##caption:Wani yaro na karbar rigakafi.##