Ministan kiwon lafiyar kasar Dr Idi Mainasara ya gargadi al’ummar kasar da su bada muhimmanci ga shayar da jarirai nonon uwa tsantsansa har tsawon watanni shida. Yace wajibin mu ne mu sanar da iyaye mata da ma’aikatar kiwon lafiya da ma’aikatar kafofin yada labarai da duk masu ruwa da tsaki a wannan fanni da a jajirce wurin tallafawa sha’anin bada nonon uwa.
Wata likita a babban asibitin birnin Kwanni ta dora muryarta a kan kira ga muhimmancin shayar da nonon uwa. Tace idan aka shayar da kananan yara nonon uwa kadai har tsawon watanni shida zasu samu kariya daga cututtuka kuma zasu samu kuzari kana su shakku da iyayensu kuma su tausayawa iyayensu.
Jamhuriyar Nijer tana kebe mako guda a duk shekara domin fadakar da iyaye a kan muhimmancin shayar da kananan yara nonon uwa kadai har tsawon watannin shida da zummar kawo karshen cututtuka da mace macen yara sababbin haifuwa zuwa shekaru biyar.
Your browser doesn’t support HTML5