Cikin manyan mutanen da suka halarci taron kaddamarwar har da mataimakin shugaban kasar Najeriya Namadi Sambo.
Yayin da yake jawabi mataimakin shugaban Namadi Sambo yace sun yi farin cikin kaddamar da jiragen wanda yace cigaba ne a kokarin gwamnati mai ci yanzu domin kawo sauye-sauyen manufofin da zasu gyara kasar. Mataimakin shugaban ne ya kaddamar da jiragen.
Janaral Martin Luther Agwai sugaban shirin S-U-R-E-P da ta saka daruruwan miliyoyin nera domin farfado da harkokin sufuri musamman jiragen kasa yayi karin bayani a wurin taron . Yace sun tabbatar yanzu jirgi na iya tafiya daga Fatakwal zuwa Enugu. Fatansu shi ne nan da dan lokaci kadan jirgin zai iya wucewa har Kafanchan. Yanzu sun kashe nera biliyan talatin da hudu da miliyan dubu dari shida.
Jama'a da dama na ta sambarka sabili da wannan cigaba da aka samu da fatan abun da aka yi zai dore.
Ga rahoton Lamido Abubakar.
Your browser doesn’t support HTML5