Mai alfarma sarkin Musulmin Sa’ad Abubakar na uku ya bukaci gwamnatin kasa da ta hanzarta binciko wadanda ke da hannun a kissan mummuken da aka yiwa Fulani makiyaya a yankin Gembu dake jihar Taraba,da kuma na kwanakin nan a Numan inda rayukan kananan yara fiye da hamsin suka salwanta. Sarkin Musulmin ya yi wannan kiran ne a jawabinsa yayin bikin kaddamar da gidan radiyon Fulfulde na farko a Najeriya wato Pulaaku FM,wanda mai martaba Lamidon Adamawa Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa ya kafa a Yola,
Mai alfarma sarkin Musulmi,wanda mai martaba Sarkin Kano,Muhammad Sanusi na biyu ya wakilce shi,yace koda yake ba zasu goyi bayan duk wani bafulatani da ke tada husuma ba,amma kuma yace yanzu sun zura ido suga matakin da gwamnatin Najeriya zata dauka game da kissan na Mambilla da kuma batun hukunta wadanda ke da hannun a kashe 'ya'yan makiyayan na Numan.
‘’Bama son a dauki hakurinmu ( fulani ), ya zama tamkar ragwanci,bin doka yasa haka,don haka yanzu mun zura ido da kasa kunne don ganin matakin da shugabanin tsaro zasu dauka na hukunta wadanda ke da hannu.Har yanzu bamu mance ba da abubuwan da suka faru a Mambilla,da kuma wanda ya faru yanzu a Numan.
‘’Don haka muna fatan ba za’a kyale wadanda ke da hannun a kashe kashen da aka yi a Mambilla da kuma na Numan din ba.’’
Shi ko a jawabinsa wakilin shugaban kasa a wajen taron wanda kuma shine ministan harkokin yada labarai,Alh.Lai Muhammad ya ma yaba ne game da rawar da kafofin yada labarai ke bayarwa wajen samar da zaman lafiya,musamman a wannan lokaci na yaki da ta’addanci Boko Haram,da yace an shawo lagwansu.
Shima dai a jawabinsa Gwamnan jihar Adamawa Sen.Bindow Jibrilla wanda yayi Magana cikin harshen fillanci ya ci alwashin gano wadanda ke da hannu a aika-aikatan da aka yi a Numan,kana ya bukaci al’umman jihar da su koyi alakar zaman tare.
Sarakuna na ciki da wajen Najeriya da dama suka hallarci bikin bude gidan rediyon da ke watsa shirye shiryensa a karamin zango na FM,koda yake yana yanar gizo.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdul'aziz ya aiko.
Your browser doesn’t support HTML5