An Kaddamar Da Cibiyar Kayan Tarihin Amurkawa Bakaken Fata

  • Ibrahim Garba

Cibiyar Kayan Tarihin Amurkawa Bakaken Fata

Shugaban Amurka Barack Obama ya jaddada cewa Amurkawa Bakaken Fata ba cima-zaune ba ne ko kadan; sun taka muhimmiyar rawa wajen gina Amurka.

Da ya ke jawabi a wurin bukin kaddamar da wata sabuwar cibiyar adanawa da baje kayen tarihin Amurka, wadda za ta fi raja'a ga tarihin Amurkawa bakaken fata, Shugaban Amurka Barack Obama ya ce tarihin Bakaken fatan wani ginshiki ne na tarihin Amurkar kanta, tun daga zamanin wadanda su ka kafa kasar.

"Mun fai mancewa da labaran da su ka shafi miliyoyin wasu mutane, wadanda su ka gina wannan kasar kamar sauran," a cewar Obama.

Obama, wanda wani sa'in sai da ya yi ta dan goge kwalla, ya yi nuni da alfanu da kuma hadarin da ke tattare da zama Bakar fata a Amurka, kama daga zamanin bauta da wariyar launin fata na Jim Crow zuwa zamanin 'yancin kada kuri'a da kuma zaben Bakar fata na farko Shugaban kasa.

"Mu fa ba wata dawainiya ba ce ga Amurka, ko kuma wani lahani gare ta ... Amurkar ce ma mu. Kuma abin da wannan cibiyar kayan tarihin ke bayyanawa kenan," abinda ya gaya ma dubban mutanen da su ka taru wurin wannan buki a dandalin taro na kasa kenan.

Bayan an shafe shekara da shekaru ana ginawa, sobuwar cibiyar kayan tarihin, wacce aka gina a dandalin kasa da ke birnin Washington DC, mai suna Cibiyar Kayan Tarihi ta Kasa ta Tarihi da Al'adar Amurkawa Bakafen Fata, an kammala tare da bude ta ga jama'a a hukumance jiya Asabar.

Wanda Moore, wadda ta halarci bukin da diyarta Celeste, ta ce, "Sau dayawa mutane ba su son magana kan zamanin bauta, to amma ina ganin abu ne mai muhimmanci saboda daga Afirka kakanninmu su ka zo, kawo su aka yi nan," Moore ta kara da cewa, "Su bayi ne kuma ba na ganin wannan wani abin kunya ne, ina ganin su na da juriya shi ya sa su ka iya kaiwa nan."