An Kaddamar Da Addu'o'in Kwanaki Uku A Tanzaniya

A yau Juma’a 17 ga watan Afirilu kasar Tanzaniya ta kaddamar da addu’o’in kwanaki uku a yayin da annobar cutar coronavirus ke karuwa.

A jiya Alhamis ne Shugaban kasar John Magufuli ya kaddamar da addu’o’in a fadin kasar, ya yi kira ga ‘yan kasar da su nemi tsari da sauki daga Allah, yayin da aka samu karin mutum 6 da suka kamu da cutar. Yanzu haka kasar na da mutum 94 da suka kamu da cutar.

Ya zuwa yanzu, mutum 4 sun mutu a sanadiyyar cutar a Tanzaniya, inda aka hana duk wani taron jama’a aka kuma rufe makarantu, amma ba a rufe wuraren ibada ba kuma mutane na ci gaba da zirga-zirga ba tare da wani sharadi ba.

Kiran gudanar da addu’o’in na zuwa ne bayan da kasar ta soke bikin ranar hutun 26 ga watan Afirilu da ake tunawa da hade yankin Tanganyika da Zanzibar wanda ya samar da kasar Tanzaniya a shekarar 1964, sakamakon barkewar annobar coronavirus.

Firai Ministan kasar Kassim Majaliwa, ya ce Shugaba Magufuli ya sauya akalar kudi dalar $217,000 da aka ware don bukin zuwa kokarin yaki da cutar coronavirus a kasar.