An kaddamar da wata sabuwar cibiyar kula da kuma killace masu cutar COVID-19 a tashar jirgin kasa dake IDU.
Wasu kamfanoni da attajirai masu kishin kasa a babban birni tarayyar Najeriya Abuja ne suka ba da tallafin kafa cibiyar don yaki da cutar COVID-19 da ke ci gaba da lakume rayukan mutane, a karkashin Kwamitin ma’aikatar babban birnin tarrayar dake ba da shawarwari kan yaki da cutar.
Ministan Birnin Tarayya Mallam Muhammad Musa Bello ya kaddamar da katafaren ginin hawa hudu da ke dauke da gadajen kwantar da marasa lafiya sama da dari biyar, da kuma na’urori na zamani.
Ministan ya ce, duk da samun kari da ake yi na masu daukar wannan cuta akwai wadanda har yanzu, ba su bin doka kuma ba su gamsu kan cewar akwai cutar ba.
Ya zuwa yanzu dai an gwada mutane sama da dubu uku a Abuja, kuma hukumar birnin tarraya na kokari wajen gannin cutar ba ta bazu a karkara ko kananan hukumomi ba, a cewar shugaban kwamitin Dr. Aliyu Moddibo Umar.
Muhammad khoury wakilin gidauniyar bankin Ja’iz da su ma suka ba da tallafi na kayyakin abinci ya ce, Irin rawar da Kungiyoyi da ma’aikatu da attajirai suka taka abin a yaba ne, kuma abin farin ciki ne idan al’umma musamman marasa karfi su ka ci moriyar tallafin.
Haj. Ramatu Tijjani Aliyu, karamar ministar birnin tararraya, wacce kuma ta ke jagorantar kwamitin da ke sa ido wajen rarraba kayyakin tallafi na abinci a karakashin kwamitin da ke yaki da cutar COVID-19, ta ce an ware wani kwamitin don tantance wadanda su ka ba da tallafi da kuma wadanda suka cancanci su kar bi tallafin.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim.
Your browser doesn’t support HTML5