An Juya Kalamun Shugaban Nigeria Akan Matasa a Saboda Wata Manufar siyasa Ne

Shugaba Muhammad Buhari

Kalamun shugaba Buhari akan matasan Najeriya da aka ce ya yi a Ingila ya jawo cecekuce abun da mai bashi shawara akan lamuran matasa ya ce juya kalamunsa aka yi saboda wata manufa ta siyasa

A hirar sa da Muryar Amurka, mai baiwa shugaban Nigeria shawara akan harkokin matasa, Nasiru Saidu Adahama ya musanta zargin cewa shugaba Muhammad Buhari ya kira matasan Najeriya cima zaune.

A cewar sa babu wata takaddama tsakanin shugaban kasa da matasan Najeriya. An canza lakamun shugaban ne domin wata manufa ta siyasa. Ya ce babu inda shugaban ya kira matasan Najeriya malalata a cikin tambayoyin da aka yi masa a Ingila da kuma amsoshin da ya bayar.

Lokcin da yake amsa tambayoyin da aka yi masa ya fada cewa Najeriya nada mutane miliyan 180 kuma kashi sittin daga cikin dari na wannan adadi matasa ne. Amma an bata tunanin matasa, ba’a nuna masu yadda zasu tashi su yiwa kansu wani abu ba sai dai su jira gwamnati ta yi masu komi ba yadda matasan kasashen da suka ci gaba ke yi ba. Wannan ko ya samo asali ne daga masu satar dukiyar gwamnati su raunata tunanin matasa. A wancan lokacin matashi ba zai tashi ya nema ba yana jiran a debo ne a bashi.

Da Shugaban kasa ya samu mulkin kasar sai ya canza tunanin matasan. Yana cewa su tashi su nema musamman ta harkar noma da kiwo domin kasar ta samu dogaro ga kanta. Gwamnatin Najeriya ta daukar wa matasan nauyin neman musu jari ko kayan aiki. Injishi bayanin da shugaba yayi ke nan amma sai aka juya aka ce ya kira matasa malalata.

Ga Medina Dauda da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Mai Ba Shugaba Buhari Shawara Akan Matasa Ya Ce An Juya Kalamun Shugaban Ne - 3' 00"