Kusan mutane 20 ne suka raunatta lokacin da daliban Jami'ar Oye-Ekiti (FUOYE) da masu 'yan okada, inda aka ce wasu daga cikin su mutanen 'yan asalin yankin ne, da suka shiga cikin tashin hankalin, yau ranar Laraba.
Mujallar Daily Post ta wallafa cewa wadanda suke tsaye a lokacin da fadan ya barke sun gayawa jaridar Daily Post cewa fadan ya fara ne kan kudin biyan dan okada inda wani dalibi da mai dan okadan suka fara musayar kalamai.
Wani ya ce ''mai tuka babbur din ne ya mari dalibin daga bisani sai fada ya barke tsakanin su, sai wasu dalibai suma suka shiga fadan. Rikicin ya kai wani mataki ne bayan masu tuka okda sun kirawo taron dangi kan daliban, waddanda suka ruruta rikicin.
Kakakin jami'iar FUOYE, Mr. godfre Bagaji, yayinda yake bayani kan rikicin, yace rikicin tsakanin daliban mu ne da 'yan okda, ya kara da cewa rikicin ya barke ne ba zato ba tsamani a wajen filin jami'ar.