An ja Kunnen Bakin Haure ko Su Yabawa Aya Zaki

Wasu Bakin Haure

Shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya, mai kulla da jihar Jigawa, Alhaji Isa Idris Jere, ya gargadi bakin haure cewa zaben dake tafe a Najeriya, bai shafe su ba saboda haka sun nisanci rumfunar zabe ko kuma su yabawa aya zaki.

Yayi wannan gargadi ne a wani taro da yayi da shuwagabanin bakin haure mazauna jihar Jigawa, yace gargadin ya zama wajibi ta la’akari da cewa a shekaran da ta gabata jami’an hukumar sun kama mutane ashirin ‘yan kasashen waje da katin hukumar zabe ta Najeriya.

Alhaji Abdulrahaman Abdu, wanda yake shine shugaban alumar ‘yan Nijer, mazauna jihar Jigawa, shine ya jagoranci sauran bakin mazauna jihar Jigawa, zuwa wajen taron.

Yace “ duk bako wanda ba dan kasa bane ba hurumishi bane ya je ya shiga harkar zabe a wata kasa, mutanen mu sun koma su kalla suyi adu’a, don zaman lafiya, shine ya kawo mu, idan kasa babu zaman lafiya, muma ba zamu zauna ba.”

Your browser doesn’t support HTML5

Bakin Haure Jigawa - 3'04"