An Inganta Na'urar iPad Ta Yadda Zata Gane Fuskar Mai Ita

An kayatar da sabuwar nau’rar iPad ta kamfanin Apple, ta yadda zata gane fuska ko kwayar idon mai ita, wannan tsari ne da zai ba masu amfani da wayar ko wadanda suka mallaki wayar damar kullewa da budewa ta hanyar kallon fuskar wayar kO iPad.

Sabon tsarin dai ya inganta wayoyi na iPhone XR da XS da fasahar, a duk lokacin da wani ya dauki wayar ba tare da yardar mai itaba, ba zai iya budeta ba harma yayi amfani da ita.

Mutun kan iya amfani da sabuwar iPad ko iPhone don biyan kudaden kaya da ya saya ko amfani da wasu manhajoji da zasu ba mutun damar biyan wadansu kudade da yake da bukatar biya, ba tare da mutum ya shigar da bayanan shi a duk lokacin da bukatar hakan ta zo ba.

Kamfanin na Apple ya kaddamar da wannan sabuwar na’urar tafi da gidanka ne a wani taron jama’a a birnin New York, inda kamfanin ya bayyana kokarin shi na cigaba da kare na’urorin ta yadda da babu wani dan kutse da zai iya yin nasara akansu.

An dai bayyanar da cewar kasuwar na’urar iPad tayi kasa, amma kamfanin na Apple ya tabbatar da cewa shi kuwa ya samu karuwar kudi ta hanyar saida waya da iPad, don kuwa a shekarar da ta gabata ya sayar da na’urar iPad akan kudi dallar Amurka milliyan arba’un da hudu.