Jami’in hukumar Mr, Vincent Mashikir ya bayyana haka cikin makalar da ya gabatar a taron karawa juna sani da ta shiryawa ‘yan jaridu tare da hadin gwiwar asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya ko UNICEF, a takaice, ta shiyar a Yola, jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya kan muhimmancin rajistan yara da aka haifa da yara ‘yan kasa da shekara biyar.
Jami’in ya ce sun shirya taron karawa juna sanin ne sakamakon tirjiya da ya gamu da shi tun lokacin da aka soma shi a shekara ta alib dari tara da casa’in da biyu a matsayin shaidar zama dan kasa wanda jihar Adamawa ke baya idan aka kwatanta ta da sauran jihohi.
Wani dan jarida da da ya halarci taron karawa juna sanin da wakilin sashin Hausa ya yi hira da shi Solomon Kumangar shugaban sashin labarai na gidan telebijan na jihar Adamawa ya ce ya karu matuka, amma ya nuna takaicinsa ga gurguwar fahimtar da wasu iyaye suka yiwa shirin, yana mai cewa zasu tsara shirye-shirye na fadakarwa a kafarsu kan muhimmancinsa wajen samarwa yara ilimi mai nagarta, kiwon lafiya da ingantattun kayan rayuwa wajen tsara ayukan rayawa na gwamnatoci .
Malama Tina Pheneas da Michael Musa cewa suka yi taron ya fadakar dasu mummunar illar rashin yiwa yara rajistar haihuwa wanda suka bayyana da ya jawowa jiha koma baya , tauye ci gaban yara da kuma cutar da rayuwarsu nan gaba.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin labari.
Your browser doesn’t support HTML5