An bindige wani babban jami'in sojin Somaliya a birnin Mogadishu da yammacin jiya Lahadi, a cewar majiyoyin jami'an tsaro ga Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka.
Wasu 'yan bindiga dauke da 'yan kananan bindigogin nan na 'pistol,' sun harbe Janar Mohammad Sheikh Qururuh da wani dogari, yayin da su ke tafiya gida daga masallaci a babban birnin na kasar Somaliya, a cewar shaidu.
Maharan sun wuce Janar Qururuh da dogarinsa, sannan sai su ka juya su ka harbe su ta baya, abin da majiyoyi su ka ruwaito shaidu na fadi kenan.
Duka mutanen biyu sun mutu nan take.
Qururuh wani babban jami'in sojan Somaliya ne a cibiyar bayar da umurnin soji a Mogadishu. A baya ya zama mataimakin kwamandan gudanarwa na sojojin Somaliya.
Nan take dai babu wanda ya dau alhakin aikata wannan kisan. An yi imanin cewa mayakan al-Shabab na da hannu a irin wadannan hare-haren da ake kaiwa kan jami'an gwamnatin Somaliya.