IAAF itace hukumar dake shirya wasannin motsa jiki na duniya, ta bada tabbacin hukuncin haramtawa hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Rasha RUSAF, shiga gasannin da take shiryawa.
Daga shekara ta 2015 ne Rasha ta fuskanci haramcin shiga wasannin na motsa jiki, bayan wani rahoto da hukumar dake yaki da shan kwayoyin karin kuzari tsakanin masu motsa jiki (WADA) ta wallafa, cewa gwamnatin Rasha na goyon bayan 'yan wasan kasar, wajen shan kwayoyin masu kara kuzari yayin da za suyi wasa.
Tun daga waccan lokacin ne aka haramtawa duk wasu masu wasannin motsa jiki, na kasar Rasha shiga gasanni amatsayin wakilcin kasarsu, sai dai zasu iya fitowa a matsayin ‘yan wasa masu zaman kansu.
Rahotannin na (WADA) ya bayyana cewa, gwamnatin kasar na da hannu dumu dumu wajen taimakawa ‘yan wasanta kan saba ka’idar wasannin na motsa jiki.
Ya zamo tilas Rasha ta amince da rahoton hukumar yaki da shan kwayoyin karin kuzari, da tayi akanta in har tana bukatar a dage mata wannan haramcin.