An Hango Garwar Jirgin Algeria da Ya Fadi a Arewa Maso Gabashin Mali

Hadarin jirgin Aljeriya, Yuli 25, 2014.

Shugaba Ibrahim Boubacar Keita na kasar Mali, yace masu bincike sun hango garwar jirgin saman kamfanin Air Algerie wanda ya bace a kan hanyarsa ta zuwa birnin Algiers daga Ougadou a kasar Burkina Faso.

Shugaba Keita yace an hangi garewanin jirgin a yankin arewa maso gabashin kasar Mali cikin hamadar dake tsakanin yankunan Aguelhoc da Kidal. Ya bayyana wannan lokacin wani taro a birnin Bamako.

Har yanzu ba a ji komai ba a kan ko akwai wadanda suka kubuta da rayukansu. Hukumomi sun ce akwai mutane 116 a cikin wannan jirgin lokacin da ya bace.

Jiraghen saman yakin Faransa dake Afirka ta Yamma sun shiga cikin masu neman inda jirgin yake. Tun da fari, ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya fadawa 'yan jarida cewa watakila jirgin nan ya fadi ne.

Akwai Faransawa 50 a cikin wannan jirgin, fiye da kowace kasa dake da fasinja ko ma'aikata a cikinsa.